Abubuwa biyar da gwamnatin Tinubu ta ƙara wa kuɗi zuwa yanzu

10 Aug 2024

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta dakatar ne ya fi girgiza 'yan ƙasar a sauye-sauyen tattalin arziki da take gudanarwaMarubuci, Daga Umar Mikail Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Sa'a 1 da ta wuce

Da - Figure 1
Photo BBC News

Babbar manufar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kamfe da ita kafin zaɓen 2023 ita ce "Sabunta Fata" ko kuma Renewed Hope a Turance. Sai dai a bayyane take 'yan Najeriya na buƙatar wani sabon fatan a yanzu sakamakon hauhawar farashin da ta biyo bayan hawansa mulki.

'Yan Najeriya ba za su taɓa mantawa da jawabin rantsuwar kama aiki na Tinubu ba a ranar 29 ga watan Mayun 2023, wanda ya ƙunshi dakatar da biyan tallafin man fetur nan take.

Tun daga nan rayuwar 'yan ƙasar ta sauya daga mai hawa zuwa mai hauhawa kusan a kowane ɓangare. Tinubu da jam'iyyarsa ta APC na cewa matakan da suke ɗauka na tattalin arziki sun zama dole, kodayake sun aminta hakan zai jawo wahalhalu na ɗan lokaci.

Hauhawar farashi a Najeriya ta kai 34.19 cikin 100 a watan Yunin da ya wuce, yayin da take a 22.79 a watan Yunin 2023 - lokacin da Tinubu ya karɓi mulki - a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa, NBS.

Cikin shekara ɗaya da wata biyu, gwamnatin tasu ta aiwatar da sauye-sauye da suka ƙunshi ƙara kuɗaɗen da ake biya ɓangarori, ciki har da na lantarki, da harajin shigo da kayayyaki cikin ƙasar.

A wannan maƙala, mun duba ɓangare biyar da gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗaɗen da aka saba biya tun bayan hawanta mulki.

Harajin shigo da kayayyaki (import duty)

A watan Disamban 2023, gwamnatin tarayya ta hannun Babban Banki ƙasar - CBN ta ƙara farashin canji tsakanin naira da dala, wanda da shi ne ake ƙiyasta harajin da ɗankasuwa zai biya na kayayyakin da ya yi safararsu zuwa cikin Najeriya.

Hakan ya sa ita ma hukumar kwastam da ke kula da safarar kayayyaki ta ɗaga farashin kuɗin da 'yankasuwa ke biya kan kayan da suka yo safara a tashoshin ruwa da na jiragen sama a faɗin ƙasar.

Rahotonni sun bayyana cewa kwastam ta sauya harajin kaya da ake biya wa ababen hawa daga naira 783 kan dala ɗaya zuwa naira 952 a lokacin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sau huɗu CBN yana ƙara farashin a 2023. A watan Yuni, CBN ya ƙara farashin canjin zuwa naira 589 kan dala ɗaya daga naira 422.30, a watan Yuli ya koma naira 770.88, sai kuma a Nuwamba da aka mayar da shi naira 783.174.

Sai kuma a watan Fabrairun 2024, CBN ya sake ɗaga darajar canjin har sau biyu cikin kwana ɗaya - zuwa naira 1,413.62.

Ƙari na baya-bayan nan shi ne na makon nan da muke ciki, inda CBN ɗin ya mayar da farashin naira 1,618.732 kan dala ɗaya daga naira 1,600.32.

'Yankasuwar da ke safarar kayayyaki na cewa hakan na nufin a yanzu harajin da za a biya wa kwantenar kaya mai tsawon ƙafa 40 zai kai naira miliyan 20, maimakon miliyan bakwai da aka saba biya a Disamban 2023.

Duk da cewa gwamnatin ta ce ta jingine harajin kan wasu kayayyakin abinci, babu tabbas ko tsarin ya fara aiki zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Kuɗin ruwa

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya naɗa Olayemi Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN a tsakiyar watan Satumban 2023, bankin ya ƙara kuɗin ruwa har sau huɗu.

Bisa tsarin harkokin kuɗi na duniya, manyan bankunan ƙasa kan ƙara kuɗin ruwa ne kan masu karɓar bashi daga bankuna da zimmar dakushe gwiwarsu wajen rage yawan bashin da suke karɓa, wanda hakan zai jawo raguwar kuɗi a hannun jama'a.

Raguwar kuɗi a hannun jama'a kuma za ta taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki. Sai dai ƙarin kuɗin CBN na musamman ne da ya sha bamban da abin da aka saba gani a ƙasashen duniya.

A zaman da kwamatin babban bankin ya yi na ranar 23 ga watan Yulin 2023, CBN ya ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 26.75 cikin 100 daga 26.25 da ya ƙara a watan Mayu.

Sai dai wasu masu sharhi na cewa lamarin dai zai ƙare ne a kan talaka mai ƙaramin ƙarfi da ke sayen kayayyakin da masu cin bashin ke sarrafawa.

Kuɗin lantarki

A ranar uku ga watan Afrilu hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta sanar da sabon farashin da abokan huldarta za su fara biya 'yan ajin Band A.

Hukumar ta ce kwastomomi za su fara biyan naira 225 kan kowane ma'auni ɗaya na wutar (unit), wanda a baya suke biyan N66.

Matakin ya jawo zanga-zanga da barazanar yajin daga haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da kuma TUC ta 'yankasuwa, kuma yana cikin dalilan da suka sa ƙungiyoyin suka yi yajin aiki na kwana ɗaya a watan Yuni.

Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ƙarin zai shafi masu samun wutar tsawon awa 20 zuwa ne kawai, kuma ta yi hakan ne saboda ta rage yawan kuɗin tallafi da take kashewa duk shekara a ɓangaren wuta.

Kuɗin man fetur

Kusan rayuwar 'yan Najeriya ta dogara ne kacokan kan man fetur idan aka kwatanta da yadda suka dogara da sufurin mota a harkokinsu na yau da kullum.

Tun kafin ya shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin, wanda gwamnati ta ce ya zame mata wani bakan-gizo da ke shanye arzikin ƙasa.

Nan take aka fara dogayen layuka a gidajen mai saboda ƙarancinsa, kuma lita ɗaya ta man ta tashi daga kusan naira 200 zuwa sama da naira 500, inda a yanzu takan kai naira 1,000 a jihohin arewacin ƙasar.

Sai dai wasu rahotonni na cewa har yanzu gwamnatin na biyan tallafin, amma ta sha musanta hakan.

Darajar naira

A ranar Laraba 15 ga watan Yunin 2023, Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da cewa ƙasar ta dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje zuwa guda ɗaya.

A baya, Najeriya na amfani da tsarin canjin kuɗaɗen waje daban-daban a hukumance, sai kuma kasuwar bayan fage, lamarin da ya sa ake samun farashin dalar Amurka iri-iri.

CBN ya kuma bai wa bankunan kasuwanci damar yin canjin kuɗi a kan farashin da kasuwa ta ƙayyade.

Duk da cewa tsarin ya yi nasarar daidaita farashi tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage na ɗan lokaci, sai dai ya sanya a hukumance darajar naira ta karye daga naira 477 a lokacin zuwa naira 750 kan dala ɗaya - yanzu ana canzar da dalar kan sama da naira 1,600 a kasuwar bayan fage.

Read more
Similar news
This week's most popular news