Me ya sa wasu jaruman Kannywood ke talaucewa bayan sun yi ...

11 Aug 2024

10 Agusta 2024

Wasu jaruman Kannywood da dama kan talauce ko su faɗa wanu hali na buƙatar taimako bayan sun ɗauki dogon lokaci suna tashe a masana’antar.

Da - Figure 1
Photo BBC News

To sai dai wasu jaruman masana’antar sun ce rashin tsari da tanadi daga wasu jaruman ne ke haddasa musu faɗawa ƙangin talaucin.

A tattaunawarsu da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, Aminu Sheriff da ka fi sani da Momoh da kuma Bashir Bala Chiroki sun bayyana abubuwan da suke ganin ke haddasa matsalar.

Bashir Bala Chiroki – wanda a shekarun baya ya yi tashe, a yanzu kuma yake fama da rayuwa, inda har ya koma sana’ar sayar da kunun aya – ya ce abin da ke haddasa matsalar shi ne rashin tanadi da tsari mai kyau.

A nasa ɓangare, Aminu Sheriff Momoh, ya ce yana kallon matsalar ta fuskoki uku, da farko ya ce ya danganta da yadda jarumi ya ɗauki sana’ar film, ‘’shin ya ɗauke ta ne a matsayin sana’a ko kuwa wani abu na nishaɗi da zai zo ya yi, ya kuma kama gabansa idan an kammala’’

‘’Abu na biyu shi ne wacce irin rayuwa ya shirya wa kansa, ya ɗauki rayuwar ne da irin ɗaukakar da ya samu masana’antar, ma’ana ya fita daga wani rukuni na mutane ya koma wani? Zai canja sutura da muhalli da ƙara kuɗin da yake kashewa ko kuma zai zauna a yadda yake?

Abu na uku shi ne wane shiri ya yi wa kansa zuwa rayuwarsa ta gaba, ‘’tun da dai ita ɗaukaka zuwa take yi kuma ta tafi, shin akwai wani tanadi da ya shirya wa rayuwarsa na yadda zai ɗora bayan gushewar ɗaukakar da ya samu a masana’antar’’, in ji Momoh.

Ya ce waɗannan su ne abubuwan da duk wani jarumi ya kamata ya yi la’akari da su bayan shigarsa Kannywood.

Ya ci gaba da cewa akwai jaruman da idan suna kan ganiyar ɗaukaka sai su ɗora wa kansu girman kai da ƙarya na sai sun canja matsayin da suke.

''Za ka ga mutum sai ya ce ruwa ma sai na gora zai sha, kuma ba zai ci abinci mai araha ba, sai mai tsada, ko ya riƙe babbar waya, ko babbar mota ko babban gida, wani ma sai ya biya kuɗi masu yawa ya kama hayar babban gida kawai saboda shi ya samu ɗaukaka'', in ji jarumin.

'Ajiye girman kai na yi na koma tallan kunun aya don nema wa kaina mafita'

Bashir Bala Chiroki – wanda ya gamu da irin wannan matsalar a baya, har ma ya koma sana’ar sayar da kunun aya - ya ce a shekarar 2019 ya shiga halin matsin rayuwa.

Ya ce shi a ganinsa matsalar shuɗewar zamani ne ta sa wasu masu shirya fina-finan suka jingine shi a gefe, daga nan kuma ya ɗauki matakin nema wa kansa mafita’

‘’Da na ga abin ba zai yiwuwa ba, sai na fitar da girman kai da kunya, na je aka koya min yadda ake haɗa kunun aya, ya yi daɗi, ya yi garɗi, don rufa wa kaina asiri, na kuma riƙa ɗauka a babur ina yi masa waƙa, haka nake yi don rufa wa kaina asiri,’ in ji jarumi Chiroki.

Jarumin ya kuma ce dama kuɗin da ake biyan jarumai a film, ba kuɗi ne da zai riƙe mutum ba, ‘’domin ba lallai ne su riƙe ka ba su kuma rufa maka asiri’’

Ya ci gaba da cewa jaruman film iri biyu ne akwai talakawa ko ‘ya’yan talakawa akwai kuma masu kuɗi ko ‘ya’yan masu kuɗi, waɗanda ke zuwa da kuɗinsu su kuma zuba jari domin shirya film.

‘’Amma su ‘ya’yan talakawa da kuma talakawan a film ɗin suke sa ran samun abin rufin asiri, don haka idan ka faɗo cikin wannan rukuni, abin da ya kamace ka shi ne ka nemi wata hanyar samun kuɗin, domin rufa wa kansa asiri,'’ kamar yadda Chiroki ya bayyana a cikin shirin Mahangar zamana na BBc Hausa.

'Ba a yin arziki da kuɗin film'

Aminu Sheriff Momoh ya ce kuskuren da wasu jaruman masana’antar ke yi shi ne shi ne shiga harkar film ne domin su yi arziki.

‘’Ba a yin arziki da kuɗin fim, duk wanda zai sa a ransa cewa zai yi arziki da abin da za a biya shi a film, to ya yi kuskure’’, in ji Momoh.

Ya ƙara da cewa arzikin da mutum zai samu a film ba ya wuce masoya waɗanda ke kallon jarumi kuma yake burgesu, su kuma suke sonsa, amma ta kuɗin da ake biya a masana’antar ba.

Ya ce babban abin da ya kamata kowane jarumi ya yi shi ne ya nema wa kansa wata sana’a ko aikin da zai dogara da kansa, koda ba a neme shi harkar film ba, to yana da sana’ar da zai dogara da kansa don ya sama wa kansa mafita.

‘’Ai ba za ka zauna tsawon wata guda ba a gayyaceka film ba, kuma kana da iyali, to me za ka ciyar da su?’’ In ji shi.

Momoh ya ce sauran ma'aikatan Kannywood waɗanda ba sa fitowa a matsayin jarumai, sun ma fi jaruman dama, saboda su suna da damar yi aiki a wasu kamfanoni ko ma'aikatu, saɓanin su jaruman waɗanda kawai fitowa suke yi a matsayin taurarin film.

Labarai masu alaƙa

'Wani lokaci kuɗin da ake biyan jarumai ko na mota ba ya isa'

Bashir Bala Chiroki ya ce abin da ake biya a film ya bambanta daga furodusa zuwa furodusa, domin a cewarsa wani furodusan zai biya isassun kuɗi saɓanin wani.

''A wani lokaci idan na yi film akan biyani naira 10,000 ko 20,000 ko 30,000, wani lokacin kuma naira 5,000 ko ma 3,000, shi fim ha babba ha ƙarami ne ya danganta da waye ya ɗauke ka''.

''Wani idan ya biya ka kuɗin film, wallahi sai ka yi wata shida kana kashewa, amma wani idan ya biya ka wallahi idan ka sake kuɗin motar komawa gidanka ma sai ka yi rance'',

''Saboda harkar film akwai riba akwai faɗuwa, wani idan ka gama masa film sai ya ce maka wane ma haɗu'', in ji jarumin.

Chiroki ya ce yana da kyau a ƙara kuɗin da ake biyan taurarin fina-finan Kannywood, kodayake a cewarsa yanzu an dan samu sauyi wasu sun fara vƙara kudin da suke biyan jarumai.

Read more
Similar news
This week's most popular news