Afirka ta Kudu: Ana fargaba kan mulkin wariya bayan kammala zaɓe

15 days ago

Ƴan ƙasar waje na fargabar cin zarafi bayan zaɓen Afirka ta Kudu

Bayanan hoto, ..Marubuci, Angela Henshall and Marta PausilliSanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, London

Sa'o'i 7 da suka wuce

Na - Figure 1
Photo BBC News

Sauyin da sakamakon zaɓen Afirka ta Kudu ya kawo, wanda zai zama wajibi ga jam'iyya mai mulki ta kafa gwamnatin haɗin gwiwa ya haifar da rashin tabbas game da makomar ƙasar.

Waɗanda suka fi shiga hali na rashin tabbas su ne ƴan ƙasar waje da ke aiki a ƙasar.

Ma'aikata ƴan ƙasar waje masu aiki a Afirka ta Kudu waɗanda BBC ta zanta da su sun ce nuna ƙyama gare su na ƙara muni a tsawon shekaru.

Cibiyar kula da ƴan cirani ta Afirka ta sanay ido kan hare-haren nuna ƙyama da suka faru a Afirka ta Kudu daga shekarar 1994.

Irin wadannan hare-hare sun kai matuƙa ne a shekarar 2008 da 2022 lokacin da aka kai wa mutum 110 farmaki.

A 2023 an kai hare-hare 63 masu alaƙa da nuna ƙyama, inda aka tarwatsa kimanin mutum 1,000.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, ƴan takara sun riƙa karkata kan abubuwan da suke nuna ƙyama ga baƙi.

Yaƙin neman zaɓe

"Abin baƙin ciki shi ne abin ya zamo wata hanyar samun ƙuri'a, idan ka kawo batutuwa na ƙyamar baƙi," in ji Marisa Lourenco, wani mai sharhi kan siyasa a Johannesburg, ya ƙara da cewa jam'iyyu da yawa sun yi hakan.

Masanin siyasar ya ce ƙarin nuna ƙiyayya kan cewa baƙi na ƙwace ayyuka yanzu ya yi ƙamari, wani abu da a baya ba ka cika ji ba, inda lamarin ya kai matuƙa a lokacin yaƙin neman zaɓe.

"Dama batun na nan a ƙasa tuntuni amma bai fito fili ba, ba ka cika jin batun ba sai a lokacin samar da tsare-tsare, amma yanzu ya zamo wata dabarar neman magoya baya ga dukkan ƴan takara," in ji shi.

Lourenco ya ce duk cewa batun ya fi shafar baƙaƙen fata ƴan Afirka, yanzu yakan shafi har baƙi da suka fito daga yankin kudu maso gabashin Asiya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, ...

‘Nuna wariya matsala ce a nan’

Na - Figure 2
Photo BBC News

Wani ɗan asalin ƙasar Ghana wanda ya fito daga Kumasi, Emmanuel Baani ya ce "Akwai matsalar nuna ƙyamar baƙi a na Afirka ta Kudu."

"A matsayinka na baƙo, dole ne ka yi ƙoƙarin kare kanka. Dole ne ka tabbatar takardunka sun cika. Dole ne ka tabbatar ka shiga ƙasar ta hanyar da ta dace, kuma dole ne ka kama kanka idan ka shigo ƙasar. Dole ne ka zamo ma'aikaci nagari."

Lokacin da ya isa Johannesburg a farkon shekarar 2014, Baani ya koma lardin Kwazulu-Natal da aiki a 2018.

Yanzu yana aiki a yankin Jozini kuma shi ne shugaban wat ƙungiyar ma'aikata ƴan asalin ƙasar Ghana.

Ya ce "Babbar matsalar da ƴan ci-rani ke fuskanta a Afirka ta Kudu shi ne na takardu. Aiki ya yi wa ma'aikatar cikin gida yawa".

Baani ya bayyana cewa akwai tarin masu neman takardun izinin aiki daga baƙi sannan kuma akwai ƙa'idoji da yawa wurin neman takardar aikin.

Ya ce abin ya shafi duk wata takardar izini da mutum ke nema, ciki har da sabon katin shaida da kuma katin izinin aiki.

Ya kuma ce babban ƙalubalen ma shi ne samun sabon aiki.

A cewar sa "Ni ɗin nan na zo ne da aikina a hannu, tare kuma da taimakon al'ummar yankin, na samu na zama tamkar ɗan gida, saboda haka ban fuskanci ƙalubale daga kowa ba, musamman ma ƴan ƙasa da ƴan ƙabilar Zulu. Suna tallafa mana a harkar aiki. Saboda haka ni ban fuskanci ƙyamar da ake yi wa baƙi ba.

"Amma mun ga tashin-tashina a wasu wuraren inda kamfanoni suka ɗauki baki aiki faiye da ƴan ƙasa".

Thomas, wani ɗan Najeriya mai karatun digirin-digirgir ya bayyana cewa tabbas akwai matsalar nuna ƙyama ga baƙi. Sai dai ya ce an fi tsauri ne a kan waɗanda ba su da takardu.

Ya ce "haka ne, harkar siyasar a yanzu cike take da ƙyamar baƙi, shi ya sa ma aka samu raguwar baƙi sosai a cikin ɗalibai".

Na - Figure 3
Photo BBC News

"Ba na goyon bayan masu shigowa ba bisa ƙa'ida ba kuma ina ganin abin da mutane suke ƙi ke nan. Akwai baƙin haure da dama a ƙasarmu."

"Ba na tunanin ko ma wane ne ya hau kan mulki zan samu matsala ni karan kaina domin na shigo ƙasar ne cikin ƙa'ida. Ina da cikakkun takardu, saboda haka babu dalilin da zai sa na yi fargaba."

Albert Mpazayabo, ɗan asalin ƙasar Rwanda, wanda ke zama da kuma koyarwa a birnin Cape Town ya ce ya ga yadda ake yin zaɓuka a lokuta daban-daban a tsawon shekara 27 na zaman shi a Afirka ta Kudu.

Ya akan yi wa ƴan gudun hijira da masu neman mafaka da kuma ƴan ci-rani kuɗin goro "inda akan ɗora duk wani laifi a kansu" ba tare da bambancewa ba.

Sannan ana alaƙanta ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta bayan ƴantuwa daga mulkin wariya a kan baƙi ƴan ci-rani.

"Babu adalci ko kaɗan kuma hakan ba ya taimakawa a ce ana ɗora laifin komai a kan baƙi".

Asalin hoton, Cosmos G. Michael

Bayanan hoto, Jam'iyyar ANC ta rasa rinjaye a majalisar dokoki a karon farko tun bayan da Nelson Mandela ya jagorance ta wajen kawar da gwamnatin wariya a 1994

Gwamnatin haɗaka?

Bayan kayen ban-mamaki da jam'iyya mai mulki ta ANC ta sha, wanda hakan ya ƙwace mata rinjayen da take da shia a Majalisar dokoki, mai magana da yawun jam'iyyar ya ce jam'iyyar na tunanin kafa gwamnatin haɗaka, inda ya ce jam'iyyar na son jam'iyyu su yi aiki tare.

Wani masani a Chatham House, Christopher Vendome ya ce wasu za su iya ganin cewa karkata wani ɓangaren baya ga kaka-gidan da ANC ta yi a baya, wani ci gaba ne.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa haɗaka ba ta cika yin kyau ba a matakin ƙananan hukumomi a Afirka ta Kudu.

Cosmos G Michael, wani ɗan ci-rani wanda a yanzu ke zama a birnin Durban na lardin KwazuluNatal ya ce bai yarda cewa gwamnatin haɗaka za ta kawo wani gagarumin sauyi ba.

Ya bayar da misali da wata takardar shawarwari da ministan cikin gida na ƙasar Dr Aaron Motsoaled ya gabatar, wadda za ta fitar da Afirka ta Kudu daga yarjejeniyar Majalisar dinkin duniya kan ƴan gudun hijira.

"Duk da cewa idan aka samar da gwamnatin haɗaka za a yi tunanin cewa za a sauya ministan na harkokin cikin gida, amma kowane ɗan ci rani na cikin shakka."

"Ni wannan babban abin damuwa ne a gare ni. Amma ba na tunanin za a samu mafi munin dokokin shige da fice fiye da waɗanda ake da su a yanzu."

Michael, wando ya je Afirka ta Kudu a 2007, wanda a yanzu yake aiki a matsayin tafinta, ya ce yana taka-tsantsan da gwamnatin haɗin gwiwa.

Ya bayyana ra'ayin jam'iyyar Patriotic Alliance da jam'iyyar Action SA kan baƙi a matsayin "mai haɗarin gaske," inda ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama ke nuna adawa da irin wannan ra'ayi.

Sai dai ya ce bai cika samun damuwa ba game da sabuwar jam'iyyar uMkhonto weSizwe (MK) da ANC da kuma DA.

"Suna da tsari game da baƙi, amma su ba haɗari ba ne ga baƙin - ba su nuna ƙyama ga baƙi." in ji shi.

Tare da gudummawar Marco Oriunto da Nomsa Maseko daga Durban

Read more
Similar news
This week's most popular news